Rahotannin da su ke fitowa daga kasashen biyu sun ce a jiya Asabar an yi musayar wuta a tsakanin masu tsaron kan iyaka, bisa zargin da Islamabad take yi wa Kabul da taimakon kungiyoyi masu dauke da makamai.
A can kasar Afghanistan kuwa majiyar tsaro ta ce ana yi fada da sojojin Pakistan akan iyakokin jahohi 7. Ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce, sun kai wa sojojin Pakistan hari akan iyakar Diyorand a matsayin mayar da martanin ta sama da Pakistan ta kai wa birnin Kabul da jahohin Khust da Nangarhar.
Pakistan tana zargin kungitar Taliban ta kasarta da kai hari daga cikin kasar Afghanistan,lamarin da Kabul take korewa.
Harin da kungiyar Taliban din Pakistan a yankin Kahibar dake kan iyaka, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23 daga cikinsu da akwai jami’an tsaro 20 da kuma fararen hula 3.
Bayanin rundunar sojan kasar Pakistan y ace; Hare-haren da kungiyar ta Taliban take kai wa sun ci rayukan mutane fiye da 500 daga cikinsu da akwai sojoji 311 da ‘yan sanda 73.