An Yi Kiran A Gudanar Da Manyan Zabukan Kasar Senegal Cikin Ruwan Sanyi

An tsara cewa za a yi zaben ne dai a ranar 25 ga watan Febrairu da ya gudana,amma shugaban kasa Macy Sall ya tura shi

An tsara cewa za a yi zaben ne dai a ranar 25 ga watan Febrairu da ya gudana,amma shugaban kasa Macy Sall ya tura shi zuwa karshen shekarar nan da ake ciki.

Sai dai kotun tsarin mulki ta kasar ta yi watsi da matakin na shugaban kasa tare da bayar da umarnin a gudanar da zaben a cikin lokaci mafi kusa.

An dauki kusan wata daya ana fama da dambaruwar siyasa a cikin kasar ta Senegal.

A yayin wannan zaben ana sa ran zabar wanda zai maye gurbin Macky Sall. Bassirou Biomaye Faye ne dan takarar adawa da magoya bayansa suke sa ran cewa zai lashe zaben.

Kasar ta Senegal tana cikin tsirarun kasashen nahiyar Afirka da suke tafiyar da tsarin demokradiyya tun daga samun ‘yanci a 1960 ba tare da soja sun tsoma baki ba.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments