An Yi Jerin Gwanon Kira Ga Kare Muhalli A Kasar Senegal

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron MDD akan muhalli a kasar Azerbaijan, matan kasar Senegal sun yi jerin gwano a birnin Dakar

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron MDD akan muhalli a kasar Azerbaijan, matan kasar Senegal sun yi jerin gwano a birnin Dakar suna masu yin kira da a yi adalci a cikin batun muhalli.

Masu fafutuka kusan 50 ne su ka halarci jerin gwanon na birnin Dakar, suna masu yin kira da kare albarkatun da kasar take da su, sannan kuma a gina rayuwa anan gaba nesa da amfani da makamashi mai gurbata muhalli.

Wani daga cikin dan fafutuka akan kare muhalli Sheik Niang Faye, ya zargi manyan kasashe masu cigaban masana’antu da gurbata muhalli, don haka ya zama wajibi su biya diyya ga sauran kasashe.

Har ila yau ya bayyana cewa, dumamar yanayin duniya yana da tasiri a cikin rayuwar yau da kullum ta mutane musamman mata a cikin karkara.

A wannan shekarar an sami ambaliyar ruwa mai tsanani a  gabashin kasar ta Senegal wanda ya lalata gonaki masu yawa da sun kai eka 1,000.

Khadi Camara ta bayyana cewa, lokaci ya yi da kasashen da suke gurbata muhalli za su rage yawan iska mai guba da manyan kamfanoninsu suke fitarwa. Domin wannan shi ne tushen barnar da take faruwa a Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments