Ma’aikatar harkokin wajen Katar ta sanar da cewa an yi karawa a tsakanin ministanta na harkokin wajen da kuma mataimakin shigaban kasar Iran akan muhimman ayyuka a birnin Davos na kasar Swissland
Sanarwar ta kunshi cewa ministan harkokin wajen kasar Katar, Abdurrahman Bin Jasim ali-Thani da kuma mai bai wa shugaban kasar Iran shawarwari na musamman akan muhimman ayyuka, Muhammad Jawad Zafir a birnin Davos na kasar Swisslanda ake yin taron tattalin arziki.
Nasarwar ta kuma ce; a yayin ganawar, bangarorin sun tattauna halin da ake ciki a Gaza da Syria.
A nashi bangaren Muahhad Jawad Zarif ya jinjinawa kasar ta Kata saboda rawar da ta taka wajen kai wag a tsagaita wutar yaki a Gaza.