Sakamakon sauyin yanayi an samu ambaliyar da ta shafi sama da mutum 700,000 a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka a wannan shekarar kawo wannan lokaci, a cewar Ofishin Bayar da Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ambaliyar ruwa ta rusa ko kuma lalata gidaje sama da 60,000, inda ta tilasta wa mutane fiye da 54,000 ciki har da mata da yara barin muhallansu, in ji OCHA a wata sanarwa da ta fitar.
Kazalika ambaliyar ruwan ta rusa makarantu da asibitoci, lamarin da ya shafi samar da ilimi da kiwon lafiya.
Sanarwar ta ce mutum 72 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu sakamakon nutsewa a ruwa sannan kusan mutum 700 sun jikkata.
Ƙasashen da ambaliyar ruwan ta shafa sun hada da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Chadi, Ivory Coast, Jamhuriyar Dimokuraɗiyya Kongo, Laberiya, Nijar, Nijeriya, Mali da Togo.