Wani bincike da kwararru kan harkokin kiwon lafiya na yahudawan Isra’ila suka gudanar ya nuna cewa an samu karuwar shan miyagun ƙwayoyi da barasa da kuma wasu dabi’u na daban a tsakanin sojojin Isra’ila, suna masu alaƙanta ƙaruwar hakan da yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza na Falasdinu.
Isra’ilawan da kamfanin dillancin labarai na AFP ya zanta da su, sun ce suna amfani da ƙwayoyin ne a matsayin wani yunƙuri na guje wa gaskiyar abin da ke faruwa da mantawa da yaƙi da kuma kawar da fargabar da suke ciki.
Masanin ilimin lafiyar ƙwaƙwlwa Shaul Lev-Ran, wanda ya kafa Cibiyar Magance Jarabar Shan Ƙwaya ta Isra’ila (ICA), ya ce “a matsayin martani na dabi’a kan damuwa da kuma neman taimako, mun ga wani gagarumin tashin hankali a cikin amfani da wasu abubuwan kwantar da hankali da ke zama jaraba. ”
Wani bincike da tawagarsa ta gudanar ya gano “dangantaka tsakanin fallasa kai tsaye ga abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba da kuma karuwar amfani da abubuwan maye” kusan kashi 25 cikin 100.
Lev-Ran ya ce ICA ta gano hauhawar amfani da “magani ba bisa ƙai’da ba da mugayen ƙwayoyi d, barasa, ko halayen jaraba kamar caca.”
A cikin 2022, ɗaya cikin bakwai na Isra’ilawa suna fama da jarabar shaye-shayen ƙwayoyi. Duk da haka, daya daga cikin Isra’ilawa hudu, tun daga lokacin, sun kara yawan amfani da kayan maye, bisa ga binciken, wanda aka gudanar a watan Nuwamba da Disamba na bara a kan samfurin wakilcin mutum 1,000 na Isra’ila.