Daruruwan matafiya ne suke zaman dirshan a filin saukar jiragen sama na kasar Tanzania saboda rikicin da ya barke sanadiyyar rikicin zaben shugaban kasa, da Samia Suluhu Hassan ta lashe da kaso 97%,kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.
An soke dukkanin tafiye-tafiyen jiragen sama da hakan ya sa matafiya na kasashen waje da dama suka makale a filayen jiragen sama saboda yanke hanyar sadarwa ta “Internet.”
Wani mtafiyi dan yawon bude ido Irvine Rene a filin suakar jiragen saman a Zanzibar ya fadawa manema labaru cewa:
” Muna kan hanyarmu ne daga nan Zanzibar zuwa Paris, amma an soke jirgin da zai kai mu zuwa Nairobin kasar Kanya, don haka mun makale a nan.”
Kasashe da dama sun gargadi ‘yan kasashen nasu da su guji zuwa Tanzania saboda halin da ake ciki na rikice-rikicen da su ka biyo bayan zabe.
“yan kasar ta Tanzania da dama sun hau kan titi suna yin Zanga-zangar kin amincewa da yadda aka gudanar da zaben, da kuma sakamakonsa da a ak fitar.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da su ka hada da MDD sun nuna damuwarsu akan mutanen da ake kashewa tare da yin kira ga mahukuntan kasar da su kaucewa amfani da karfi.
Babban magatakardar MDD Antonio Gutrress ya bayyana damuwarsa akan abinda yake faruwa, yana mai yin kira ga hukuma da kuma ‘yan hamayya da su kaucewa rikici.