An Sake Dage Babban Zaben Sudan Ta Kudu

Zaben wanda shi ne na farko a tarihin kasar, da ta sami 'yancin kai a 2011, dama an riga an dage shi sau biyu a

A Sudan ta Kudu, an dage babban zaben kasar da aka tsara gudanarwa a ranar 22 ga Disamba zuwa 11 ga Fabrairun shekara mai zuwa ta 2027.

Zaben wanda shi ne na farko a tarihin kasar, da ta sami ‘yancin kai a 2011, dama an riga an dage shi sau biyu a 2022 da 2024.

Yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 ta tanadi zaben gama gari bayan yakin basasar da ya barke ​​a 2013 tsakanin sojojin Shugaba Salva Kiir da na abokin hamayyarsa, Riek Machar.

Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma ba a aiwatar da ita yadda ya kamata ba, kuma rashin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar, Wanda ake ganin wannan sabon dage babban zaben ba abin mamaki ba ne.

Hukumar Zabe ta kasar da kanta ta ambaci wahalhalun da take fuskanta, musamman na kudi.

A watan Satumba, Hukumar ta ce ta sami dala miliyan 25 kacal daga cikin dala miliyan 250 da ta ce tana bukata don shirya zaben.

Matsalar tsaro da ta tabarbare ta ci gaba da kawo cikas ga shirye-shirye.

Tunda farko dama Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗi game da raunin da Sudan ta Kudu ke da shi kafin zaben shugaban kasar dake tafe..

A watan Satumba, Shugaba Salva Kiir ya rusa gwamnatin hadin kan kasa, inda ya sallami dukkan mataimakan shugaban kasa, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa na Farko Riek Machar, sannan ya kafa gwamnatin wucin gadi.

‘Yan adawa a kasar sun yi watsi da wadannan matakai, suna kallonsu a matsayin karya ka’idojin raba iko da aka tanada a yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted