An saka dokar Ta Baci  Bayan Barkewar Zanga-zanga A Zaben Shugaban Kasar Tanzaniya

Ƴan sanda a kasar Tanzania sun saka dokar hana zirga-zirga a fadin kasar bayan zanga-zangar da ta barke yayin zaben shugaban kasa da ya rikide

Ƴan sanda a kasar Tanzania sun saka dokar hana zirga-zirga a fadin kasar bayan zanga-zangar da ta barke yayin zaben shugaban kasa da ya rikide ya koma tashin hankali a wasu sassa daban-daban na kasar.

Rahotanni sun nuna cewa, zanga-zangar ta barke ne musamman a birnin Dar es Salaam da wasu garuruwa yayin da jama’a ke nuna rashin jin daɗi kan yadda ake gudanar da zaben shugaban kasar.

Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya a tsarin zaben, kuma sun  nemi  gwamnati ta gyara tsarin zabe da kuma ba kowa damar fadin albarkacin baki.

A cewar jami’an tsaro, an sanya dokar ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sai dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayyana damuwa cewa wannan mataki na iya kara takura ’yancin jama’a musamman a lokacin da ake jiran sakamakon zaben shugaban kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments