An Sace Daliban Jami’a Fiye Da 20 A Jihar Benuwe Najeriya

Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a wannan Juma’ar ta tabbatar da sace ɗalibai fiye da 20, tana mai cewa lamarin ya faru ne a kan

Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a wannan Juma’ar ta tabbatar da sace ɗalibai fiye da 20, tana mai cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Otukpo zuwa Enugu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene Anene ce ta sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin Makurdi.

SP Anene wadda ba ta yi wani ƙarin bayani ba, ta ce “lamarin ya faru kuma muna gudanar da bincike.”

Sai dai SP Anene ta ce waɗanda lamarin ya rutsa da su suna tafe ne a cikin wasu motocin bas biyu da misalin karfe 6.00 na yamma bayan sun ƙetare Otukpo a ranar Alhamis.

Daliban jami’o’in biyu sun gamu da tsautsayin ne bayan ’yan bindigar sun tare musu hanya suna ƙoƙari ƙetarewa ta Jihar Benuwe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, fiye da ɗalibai 20 da lamarin ya rutsa da su suna karatu ne a fannin nazarin kiwon lafiya da ke kan hanyarsu ta halartar taron ɗalibai ’yan ɗariƙar katolika da ke nazari a fannin likitanci da za a gudanar a Jihar Enugu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments