An Nada Tsohon Shugaban ‘Yan Tawayen Siriya A Matsayin Shugaban Gwamantin Rikon Kwaryar Kasar

An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun

An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya

Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar.

Tun a jiya Laraba ce, shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Ahmed al-Sharaa (al-Jolani) ya gabatar da jawabi na samun nasara bayan ganawa da shugabannin bangarorin soja a birnin Damascus fadar mulkin kasar, a gaban dandazon bangarori da dakarun Siriya.

A yayin jawabinsa na nasara, Al-Sharaa ya ce: A yau kasar Siriya tana bukata abubuwa fiye da kowane lokaci, yana cewa, kamar yadda suka kuduri aniyar ‘yantar da kasar a baya, wajibi ne su kuduri aniyar gina ta da raya ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments