An Nada Tsoffin Shugabannin Najeriya, Kenya, Da Ethiopia Domin Shiga Tsakani A Rikicin Congo

A kokarin da ake yi na shawo kan rikicin kasar Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, an nada wasu daga cikin tsoffin shugabannin kasashen Afirka a matsayin masu

A kokarin da ake yi na shawo kan rikicin kasar Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, an nada wasu daga cikin tsoffin shugabannin kasashen Afirka a matsayin masu shiga tsakani domin warware rikicin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin ta Dimokuraɗiyyar Congo.

Hakan kuwa yana zuwa ne bayan da Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) suka yanke shawarar daukar wanan mataki, inda suka nada tsoffin shugabannin Najeriya, Kenya da kuma Ethiopia domin sanya ido a kan batun sulhu a rikicin Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo wanda kullum yake kara ta’azzara, duk kuwa da yarjeniyoyin suhu da dama da aka rattabawa hannu.

Wadannan kungiyoyi sun nada tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha, Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo domin ganin sun taimaka saboda tabbatar da sabuwar yarjejeniyar da kuma yin aiki da ita.

Bangarori na kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da kuma ita kanta Tarayyar Afirka, sun dauki tsawon shekaru suna fadi tashin ganin sun kawo kan wannan matsala ta Congo, amma lamarin ya ci tura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments