Rahotanni da dama na nuni da cewa kimanin sojojin Isra’ila 7 ne aka kashe a kudancin kasar Lebanon yayin arangama da kungiyar Hizbullah ta kasar.
An kuma jikkata sojoji 21 a yayin arangamar, wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
A halin da ake ciki sojojin Isra’ila sun haramtawa duk kafafen yada labaran da abin ya shafa fallasa bayanan da suka faru.
A cewar rundunar sojojin kasar 61 ne aka jikkata a kudancin kasar Lebanon cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a kuma, rundunar sojin kasar ta sanar da cewa an kashe dakarunta 10 a fadan da aka gwabza a kudancin kasar Lebanon cikin sa’o’i 48 da suka gabata.