An Kama Masu Zanga-Zangar Adawa Da Ziyarar Trump A Philipine

jami'an yan sanda a kasar philipine sun kama dubban masu zanga zangar nuna adawa da ziyar trump

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomi a kasar philiphine sun kama akalla mutane 300 adadai lokacin da dubban masu zanga-zanga suka cika manyan titunan birnin manila domin nuna adawa da ziyarar da shugaban Amurka Donald trump ya kawo kasar,

A jiya ne shugaban Amurka ya isa birnin manila don halartar taron koli na kungiyar ASEAN da hakan ya janyo zanga- zanga kan manufofin gamnatinsa na koma bayan tattalin arzki daga yakin Amurka da Isra’ila kan iran, da kuma wani shiri da Amurka ke jagoranta kan fasahar kere-kere  da ma’adinai masu muhimmanci

Masu shirya zanga-zangar sun ce akwai mutane dubu 10 da ake saran za su halarcin zanga-zangar da nufin yin maci zuwa babban dakin taro na philiphine inda ake gudanar da taron kolin, sai dai jami’an yan sanda sun dakile yunkurin da masu zanga-zangar suka yi na yin dafifi a gaban dakin taron

Masu zanga-zangar sun rika rera taken cewa tromp ya fita, suna kira da shugaban kasar Amurka ya fice daga kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted