An kaddamar da babbar cibiyar Tallafawa Dalibai ta Duniya don Falasdinu (GSPN) a birnin New York da nufin inganta hadin gwiwar duniya domin taimakon Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya bayar da rahoton cewa, wannan cibiyar sadarwa ta kunshi daruruwan kungiyoyin dalibai daga jami’o’i daban-daban na duniya, wadanda suka hada da na Amurka, Turai, Afirka da wasu kasashen Larabawa da na musulmi.
Dalibai masu fafutuka, kungiyoyin dalibai da kungiyoyin da ke goyon bayan Falasdinu sun yi kokarin wajen kafa da kuma kaddamar da wannan cibiya ta “Global Student Network for Palestine Support” (GSPN) don ga ci gaban yunkurin kasa da kasa na goyon bayan Falasdinu da kuma yunkurin ganin an dakatar da yakin Isra’ila kan Gaza, tare da yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ke yi a Gaza, da kuma yunkurin kauracewa saka hannun jarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a jami’o’i.
Cibiyar sadarwa ta sanar a cikin wani sako cewa za ta samar da wani tsari na aminci da lamuni ga masu fafutuka na dalibai don musayar dabaru da inganta hadin gwiwa a duniya, kuma hakan zai hada da tallafawea masu fafutuka na daliban Falasdinu.
Sanarwar ta kuma ce, cibiyar tana kokarin samar wa daliban da ke goyon bayan Falasdinu, musamman wadanda ke cikin al’ummomi masu nisa ko kuma suke a gefe da kayan aiki, tallafi da kuma ilimin da ake bukata don aiwatar da ingantattun dabaru da kuma kara tasirinsu a cikin al’ummominsu.
Shugabannin daliban wannan cibiyar sadarwa sun bayyana cewa, sun himmatu wajen karfafa muryar Falasdinawa a matakin duniya, da mayar da hankalin duniya kan gwagwarmayar Palastinawa, tare da karfafa fafutukar tabbatar da adalci, tare da samar da wata cibiyar hadin gwiwa ta dalibai masu fafutuka a duniya.
Wannan rukunin yanar gizon ya nemi jami’o’in da su fuskanci ayyukan gwamnatin mamaya ta Isra’ila tare da tallafawa ‘yancin dalibai na yin zanga-zangar, da kuma kawo karshen duk wata dangantaka da cibiyoyin ilimi da bincike na gwamnatin Isra’ila da kuma janye hannun jari a duk kamfanoni da tallafawa Isra’ila.
Har ila yau, wannan cibiyar sadarwa ta yi kira ga daukacin masu fafutuka, kungiyoyi da abokan hadin gwiwa da su shiga wannan yunkuri, wanda a wannan mataki na tarihi wani muhimmin bangare ne na yunkurin tabbatar da adalci a duniya, kuma a sahun gaba wajen hadin kan duniya domin mara baya ga al’ummar Palastinu.