An Gudanar Da Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Kasashe 6 Na Nahiyar Turai A Jiya Asabar

An gudanar da zanga zangar goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza, a birane da dama a kasashen turai kimani 6 a jiya Asabar. Kamfanin dillancin

An gudanar da zanga zangar goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza, a birane da dama a kasashen turai kimani 6 a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya bayyana cewa dubban daruruwan mutane, masu goyon bayan Falasdinawa, wadanda kuma suke bukatar a dakatar da yakin da ke faruwa a Gaza sun fito kan tituna a biranen Manchester da Lodan na kasar Burtania.

Sannan wasu dubban sun fito kan tituna a biranen  Orhus da Copenhegan na kasar Denmark, sai kuma garuruwan Rotterdam da Amstruderm na kasar Holan. Sannan mutane sun fito kan tituna a wasu birane a kasar Sweden, duk sun fito don nuna fushinsu kan kissan kiyashin da ke ci gaba a yankin zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Hakama a kasar Jamus da birnin Paris na kasar Faransa dubban mutane sun fito suna All..wadai da goyon bayan da gwamnatocin kasashen yamma suke bawa HKI. Sun kuma bukaci a kawo karshen kissan kiyashin da ke faruwa a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Ya zuwa yanzu dai sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa akalla dubu 39.5 a gaza, a yayinda wasu fiye da dubu 91 suka ji Rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments