An gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da Isra’ila a  Afirka ta Kudu

Al’ummar kasar Afirka ta kudu sun yi zanga-zangar la’antar Haramtacciyar Kasar Isra’ila a biran fadin kasar Masu zanga-zangar sun fito kan titunan babban birnin kasar

Al’ummar kasar Afirka ta kudu sun yi zanga-zangar la’antar Haramtacciyar Kasar Isra’ila a biran fadin kasar

Masu zanga-zangar sun fito kan titunan babban birnin kasar Afirka ta Kudu, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu da Labanon, a daidai lokacin da ake cika shekara guda da kaddamar farmakin Aqsa. Masu shirya zanga-zangar sun kuma mika wata takarda ga majalisar dokokin kasar, inda suka bayyana adawarsu da zaluncin  “Isra’ila.”

Masu zanga-zangar dai sun daga tutoci Falastinu domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu da Lebanon, suna rera taken yin Allah wadai da zalunci da laifukan da “Isra’ila” ke aikatawa kan kasashen biyu.

Zanga-zangar wacce kungiyar hadin kai domin goyon bayan Falastinu ta shirya, ta kunshi daga tutocin Falastinu, da hotunan na wasu daga cikin fararen hula da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa kisan gilla.

Masu zanga-zangar sun bayyana matukar goyon bayansu ga korafin da Afirka ta Kudu ta yi kan “Isra’ila” da ta mika wa kotun kasa da kasa, inda suka zarge Haramtacciyar Kasar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a Gaza.

Masu shirya taron sun gabatar da wata takarda ga Majalisar Dokokin Afirka ta kudu, inda suka bukaci gwamnati da ta aiwatar da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ta shekarar 1973 kan kawar da duk wani nau’i na nuna wariya, wanda hakan ya bayar damar daukar matakan  kauracewa “Isra’ila”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments