An Gayyaci Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Aragchi Taron Makamashin Nukliya A Amurka

Bayan taro na biyu tsakanin JMI da Amurka a birnin Roma na kasar Italiya a jiya Asabar an gayyaci ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas

Bayan taro na biyu tsakanin JMI da Amurka a birnin Roma na kasar Italiya a jiya Asabar an gayyaci ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi don gabatar da Jawabi a wani taro wanda mahukuntan kasar Amurka suka shirya.

Kamfanin dillancin labarai IP na kasar ya nakalto masu shirya taron na cewa an gayyace Abbas Arichi don gabatar da  jawabin ne don muhuntan Amurka su ji ta bakin wadanda suka kore a sanin amfanin makamashin nukliya ta zaman lafiya da kuma tattaunawa a kansa.

Labarin ya nakalto wadanda suke gudanar da taron wato ” The Carnegie International Nuclear Policy Conference” wanda za’a fara a gobe litinin, na cewa taron yana taimakawa mahukuntan kasar Amurka sanin kan yadda jami’an diblomasiyya yakamata su fahinci abubuwan da suke da sarkakiya a cikin fasahar nukliya.

Har’ila yau ana son jin yadda Iran take gudanar da shirin ta makamacin Nukliya ta zaman lafiya a duk tsawon shekarun da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa mai yuwa ministan ya halarci taron ta hotunan bidiyo daga nan Tehran. Labarin ya kammala da cewa taron Amurka da Iran dangane da shirinta na makamashin Nukliya da aka kammala a birnin Ruma ne ya tada wannan bukatar ta jin bangaren Iran dangane da fannonin da ake sarrafa makamashin nukliya ta zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments