An Ga Sojojin Ruwa Na Amurka A Kasar Puerto Rico A Shirinta Na Mamayar Venezuela

An ga jiragen ruwan yaki da kuma jiragen sana na yaki na Amurka Ponce, da kuma Puerto rico a jiya talata, wanda yake kara tabbatar

An ga jiragen ruwan yaki da kuma jiragen sana na yaki na Amurka Ponce, da kuma Puerto rico a jiya talata, wanda yake kara tabbatar da Shirin Amurka na mamayar tada rikici a yankin Caribian musamman kuma a kasar Venezuela.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar iran ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Trump tana kara yawan sojojinta a kudancin Amurka musamman kusa da kasar Venezuela da nufin kifar da gwamnatin Shugaba Nicolas Madoro. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu kasashen yankin kudancin Amurka da dama suna tunan makamarsu idan har shugaban Trump ya sami nasarar aiwatar da shirinsa na kwace iko da kasar Venezuela. Saboda ba’a san inda zai dosa bayan kasar Venezuela ba. Gwamnatin kasar Venezuela dai ta bayyana samuwar sojojin Amurka a ruwayen kasashen da suke kusa da ita a matsayin tsokana, kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments