Yan takarar zaben shugaban kasa a Senegal sun kaddamar da yakin neman zabensu a ranar Asabar, kwana biyu bayan da kotu ta tabbatar da cewa za a gudanar da zaben kasar a ranar 24 ga watan Maris.
Yan takaran zaben shugaban kasar su 19 na da nan da kasa da mako uku domin shiga lungu da tsako na kasar don su nemi goyon bayan jama’a.
Wannan na nufin kuma a karon farko, za a gudanar da yakin neman zabe a cikin watan Ramadana a kasar wadda Musulmai ne suka fi rinjaye a cikinta.
Ana yi wa Senegal kallon kasa mai kyakkyawar dimokuradiyya a Yammacin Afirka.
Amma dage zaben da ya kamata a gudanar a watan fabarairu da ya gabata da shugaban kasar Macky Sall,ya yi, ya sanya rudani a kasar.
Dage zaben ya kuma jawo zanga-zangar wadda har ta rikide ta zama tarzoma.
To saidai daga bisani Kotun Tsarin Mulkin kasar ta yanke hukunci kan cewa dole ne a gudanar da zabe kafin wa’adin Sall ya kawo karshe a ranar 2 ga watan Afrilu.