An bude wani sabon zagaye na tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine a birnin Abu Dhabi na UAE a shiga tsakanin Amurka.
Shugaban tawagar Rasha, Vladimir Medinsk, kafin fara tattaunawar ya bayyana fatansa na ganin tattaunawar ta kai ga samar da zaman lafiya.
Rasha na fatan tattaunawar za ta taimaka wajen ci gaba da warware rikicin Ukraine domin amfanin mutanen Rasha da Ukraine, in ji Medinsky.
Ya kuma gode wa Hadaddiyar Daular Larabawa saboda karimcin da suka nuna, da kuma Amurka saboda kokarin da take yi na samar da zaman lafiya.
Kasashen Jamus, Burtaniya, Faransa, da Italiya suna cikin wakilan daga kungiyar Tarayyar Turai da suka halarci tattauanwar ta Abu Dhabi ta ranakun 10 da 11 ga Nuwamba, amma waɗanda ba za su kasance a teburin tattaunawa ba.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya shaida wa manema labarai a lokacin ziyararsa a Paris cewa dole ne Rasha ta amince da garantin tsaro ga Ukraine da zarar rikicin ya kare.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tattaunawar bangarori uku kan Ukraine a Abu Dhabi dama ce ta samar da ci gaba, a wata hira da Reuters, yana mai cewa zai iya kawo karshen rikicin “nan ba da jimawa ba.”