Search
Close this search box.

An Fara Taron Kungiyar Kasashen Musulmi A Kasar Gambiya

An bude taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC a birnin Banjul na kasar Gambia a yammacin afirka a yau Asabar. Kamfanin dillancin labaran IP na

An bude taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC a birnin Banjul na kasar Gambia a yammacin afirka a yau Asabar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran  ya bayyana cewa taron wanda shi ne karo na 15 ya sami halattan shugabannin kasashen, gwamnatoci da kuma manya manyan jami’an gwamnatin kasashen kungiyar.

Daga JMI Ministan harkokin wajen kasar Amir Hussain Abdullahiyan da tawagrsa ne suka wakilci kasan.  Kuma a jawabin da ya gabatar a taron na kwanaki biyu ya tabo maganar yaki a Gaza, da kuma bankin raya kasashen musulmi wato Islamic development bank IDB.

Sauran shuwagabannin kasashen  kungiyar sun tattauna yi Magana dangane da yaki a Gaza da kuma matsalolin da suke addabar kasashen musulmi a duniya.

Ana saran a karshen Taron kungiyar zata fidda bayanai daban daban, daga ciki har da matsayin kungiyar a yakin kare dangi wanda HKI take yi a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments