An Fara Taron Francophone Na 20Th A Kasar Cambodia

An bude taron kasashe renon kasar Faransa karo na 20TH a birnin Phnom penh babban birnin kasar Cambodia, a  jiya Lahadi sannan taron ya maida hankali

An bude taron kasashe renon kasar Faransa karo na 20TH a birnin Phnom penh babban birnin kasar Cambodia, a  jiya Lahadi sannan taron ya maida hankali wajen zaben sabon shugaban kungiyar.

Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa, taron ya sami halattar shuwagabnnin kasashen kungiyar da kuma manya manyan jami’an gwamnatin wasu kasashe har kimani 80 masu magana da harshen faransanci.

Labarin ya ce taron na kwanaki biyu ya fi maida hankali kan zaben shugaban kungiyar na gaba, wato DRC ko kuma Rwanda. A yau litinin ne ake saran kungiyar kasashe renon kasar Farasa ko masu magana da harshen faransanci suke zasu zabi sabon babban sakataren kungiyar wanda zai rike mukamin har na tsawon shekaru 4 masu zuwa.

Yan takarar babban kujerar shugabancin kungiyar ya hada da Louise Mushikiwabo na kasar Rwanda da kuma  wanda ya jagoranci kungiyar har na tsawon shekarau 8, wanda kuma yake son wa’adi na 3, sai sai gwamnatin kasar DRC tana adawa da wa’adinsa na uku ta kuma yi barazanar ficewa daga kungiyar idan an sake zaben Mushikiwabo, sannan kinshsha tana goyon bayan dan takararta Juliana Lumumba, diyar jarumin kasar Patric Lumumba, amma tace zata janye dan takararta idan Rwanda ta yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted