An Fara Shari’ar Masu Yunkurin Juyin Mulki A Kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango

‘Yan kasashen Amurka da Birtaniya sun gurfana a gaban kotu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango kan tuhumar hannu a yunkurin juyin mulki a kasar Fiye da

‘Yan kasashen Amurka da Birtaniya sun gurfana a gaban kotu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango kan tuhumar hannu a yunkurin juyin mulki a kasar

Fiye da mutane 50 ne ake tuhuma da suka hada da 6 ‘yan asalin Amurka da Birtaniya da Canada da kuma Belgium, wadanda suka gurfana gaban kotu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a ranar Juma’ar da ta gabata, kan zargin hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, da kuma wasu laifukan da suke dauke da hukuncin kisa.

A ranar 19 ga watan Mayu ne wasu mutane dauke da makamai suka mamaye ofishin shugaban kasa a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango na wani lokaci kafin jami’an tsaron kasar su kashe shugabansu na siyasa dan asalin kasar ta Kwango Christian Malanga da ke zaune a kasar Amurka. Wadanda ake tuhumar sun hada da dan Malanga mai shekaru 22 a duniya, Marcel Malanga, da wasu ‘yan kasar Amurka biyu da wasu mutane uku da ke da fasfo na kasashen waje, wadanda dukkansu ‘yan asalin kasar Congo ne. An gudanar da ranar farko ta shari’ar karkashin kotun soji a wani tanti a farfajiyar gidan yari na Ndolo da ke wajen birnin Kinshasa. Wadanda ake tuhuman sun sanya rigar gidan yari mai launin shudi da rawaya sannan suka yi layi a gaban alkali. Dukkanin mutane 53 na fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da mallakar haramtattun makamai, da hada baki domin aikata laifukan ta’addanci, da yunkurin kawo cikas ga harkokin cibiyoyin gwamnati da kuma rusa amincinsu, wanda wasu daga cikinsu na iya fuskantar hukuncin kisa ko kuma hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments