An Dage Zaben Sakataren Kungiyar OIF Da Shekara Guda

An dage zaben ne saboda takkadamar dake tsakanin DRC da Rwanda.

An dage zaben babban sakatare Janar na kungiyar kasashen dake amfani da harshen faransanci ta OIF, da shekara guda sabdoa rashin cimma matsaya.

Bayanai sun ce an dage zaben ne saboda takkadamar dake tsakanin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da Rwanda.

Yankuna da gwamnatoci mambobi 53 na OIF (daga cikin kasashe 90 na kungiyar) sun yanke shawarar kada kuri’a cikin sirri kuma sun amince kara wa’adin shekara guda don nemo dan takara da aka amince da shi sosai.

‘Yar kasar Rwanda, Louise Mushikiwabo, wacce ke takara a wa’adi na uku, za ta ci gaba da rike mukaminta har sai an gudanar da sabon zabe, wanda Rwanda ba za ta tsayar da dan takara ba.

Jamhuriyar DRC, wacce ke zargin Rwanda da goyon bayan kungiyar ‘yan tawaye masu dauke da makamai ta M23 a lardunan gabashinta, ta yi barazanar janyewa daga kungiyar idan aka sake zabar Louise Mushikiwabo, wacce ke rike mukamin tun 2018, a matsayin sakatare Janar na kungiyar.

Ficewar DRC da ta kasance ta biyu mafi yawan al’umma masu magana da harshen Faransanci da mutane (Miliyan 57.3) bayan Faransa zai girgizar kungiyar ta OIF, wadda ta riga ta raunana sakamakon ficewar kasashe uku na Sahel a bara (Burkina Faso, Mali, da Nijar).

Wadanda suka jagoranci kungiyar tun bayan kafa ta a 1997 sun hada da Boutros Boutros-Ghali, Abdou Diouf, Michaëlle Jean, da Louise Mushikiwabo.

‘Yan takara hudu ke fafatawa a mukamin Sakatare Janar na kungiyar da suka hada da: Louise Mushikiwabo ta Rwanda mai neman wani wa’adi; Juliana Lumumba ‘yar Congo, ‘yar Patrice Lumumba, fitaccen mai fafutukar yaki da mulkin mallaka; da tsohon FiraMinistan Romania Dacian Ciolos; da kuma tsohon Ministan Mauritania Coumba Bâ.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted