Amurka Ta Sayi Man Jiragen Sama Fiye Da Ganga Miliyan 2 Daga Matatar Dangote A Watan Maris

Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne

Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris.

Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar.

Duba daga  rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan watan na Maris.

Wani jirgin ruwa, Hafnia Andromeda, ana kyautata tsammanin zai isa tashar Everglades a ranar 29 ga Maris tare da kusan ganga 348,000 na man jirgin sama daga matatar Dangote.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments