A wani mataki na nuna goyon baya ido rufe ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi na tsawon watanni fiye 7 a kan al’ummar yankin zirin Gaza da aka yi wa kawanya, gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta yi nuni da cewa, hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai kan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a kudancin birnin Rafah, bai sabawa ka’ida ba. kuma ba zai haifar da canji a manufofin Washington game da Tel Aviv ba.
A cikin jawabai daban-daban da wasu jami’an gwamnatin Amurka suka yi sun bayyana kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Rafah a matsayin “mai raɗaɗi” amma sun yi iƙirarin cewa harin wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa fararen hula da dama, hari ne ta sama kawai, ba wani gagarumin farmaki ba ne aka kai.
A wani taron manema labarai a ranar Talata, wani jami’in Pentagon ya ce harin na ranar Lahadi, wanda shi ne mafi muni a Rafah, tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da farmaki a can, bai kai abin da fadar White House za ta yi gargadi a kai ba.