Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza.
A bukatar da aka mika wa mai gabatar da kara na kotun ICC Karim Khan a ranar 19 ga watan Janairu, 2025, wacce ta bayyana a ranar Litinin, kungiyar mai zaman kanta ta Democracy Now for the Arab World (DAWN) ta zargi Biden, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, da sakatarensa na tsaro, Lloyd Austin, da taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza.
A cewar kungiyar mai zaman kan ta, ana kuma zarginsu da bada gudummuwarsu da gangan wajen aikata wadannan laifuka.
Takardar ta nuna goyon bayan gwamnatin Biden na soja, siyasa ga laifukan Isra’ila, wadanda suka hada da jigilar makamai da suka kai dala biliyan 17.9 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, musayar bayanan sirri da kariyar diflomasiyya, kamar kin amincewa da kudurin tsagaita wuta da yawa a Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro.
“Akwai kwararan dalilai na bincikar Joe Biden, Antony Blinken da Lloyd Austin saboda hadin kai a cikin laifukan Isra’ila,” in ji mamban kwamitin DAWN Reed Brody a cikin wata sanarwa, yana mai cewa: “Bama-baman da aka jefa kan asibitocin Falasdinu, makarantu da gidajensu, na Amurka ne, kuma an gudanar da yakin da kisa da zalunci tare da taimakon Amurka. »