Tsadar man fetur ya takurawa mutanen Amurka saboda rufewar da Iran ta yiwa mashigar ruwa ta Hurmuz, a kuma dai dai lokutan zaben yan majalisar dokokin kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, a cikin watan Fabrayrun shekara ta 2026 ne shugaban Trump da kuma Firai ministan HKI suka farwa kasar Iran da yaki danun kifar da gwamnatin kasar amma suka kasa, sannan sojojin Iran suka kwace iko da mashigar ruwa ta Hurmuz inda akalla kasha 20% na makamashi yake shiga kasuwannin duniya, amma ta kasa samun nasarar yin hakan.
Trump yayi kokarin bude mashigar ruwa ta Hurmuz da karfin soje amma ya kasa yin haka. A yau watanni kimani 8 kenan da fara yakin farashin gas ko man fetur a Amurka sai kara tsada yake yi.
Tashar talabijan ta NBC News ya makalto kungiyar motocin haya ta AAA tana fada a jiya Asabar kan cewa, farashin ko wani gallon ya kai $4 a wasu yankun. Wanda ya karu da $1 kafin yakin .
Kididdiga ya nuna cewa a wasu jihohin Amurka wadanda suka hada da
California, Hawaii, Nevada, da Washington, farashin gallon guda na gasoline ya kai $5. A jimilla dai Amurkawa sun yi asarar dalar Amurka biliyon $70 saboda yakin da Amurka da HKI suka kaiwa kasar Iran.
Trump ya rasa binda zai fadawa mutanen Amurka a yakin neman zaben da yake yi idan an tambayeshi dalilin tsadar man fetur da kuma abinda ya say a fara yaki ba tare da shiri ba.