MAfi yawancin mambobin kwamitin tsaron sun yi tir da harin da sojojin HKI su ka kai wa mutanen Gaza a cikin daren shekaran jiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar fiye da Falasdinawa 400.
Wakilin kasar Rasha a MDD ya bayyana cewa; Sake bude yaki a Gaza, yana nufin korar Falasdinawa daga kasarsu” ya kuma jaddada cewa; “ Wajibi ne ga kwamitin tsaro ya yi duk abinda zai iya yi, domin sake tsayar da wutar yaki, bai kuma kamata a ce an sake maimaita kurakuren baya ba.
Shi kuwa wakilin kasar Aljeriya a MDD, ya bayyana ya zargi HKI da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, yana mai jaddada cewa; Wannan lokaci ne da hukunta masu laifi, domin babu wanda ya fi karfin doka.” Haka nan kuma ya ce; Yanzu duniya ta daina kawar da kanta daga laifukan da ‘yan mamaya suke yi.”