Search
Close this search box.

Ambaliyar Ruwa Ta Wurga Mutane Fiye Da Rabin Miliyan Cikin Halin Kaka-Ni Ka Yi A Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Rabin miliyan na ‘yan Sudan ne suka shiga halin kaka-nika yi sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa Ofishin kula

Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Rabin miliyan na ‘yan Sudan ne suka shiga halin kaka-nika yi sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya sanar da cewa: Kimanin mutane rabin miliyan ne a Sudan, ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya wurga su cikin mummunan halin rayuwa tun daga watan Yunin da ya gabata.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniyan ya kuma jaddada cewa: Alkalumman da aka tattaro suna nuni da cewa, mutane 491,100 (na iyalai 88,600) ne ruwan sama da mamakon ruwan sama ya ritsa da su a yankuna 63 da suke cikin jihohi 15 na kasar Sudan tun daga farkon fara saukan ruwan sama a watan Yunin da ya gabata.

Ofishin ya kara da cewa: Wannan ya hada da kimanin mutane 143,200 da suka yi gudun hijira daga muhallinsu. Kamar yadda jihohin da lamarin ya fi shafa suka hada da Arewacin Darfur, Bahar Maliya a gabas, Darfur ta Kudu a yamma da kuma kogin Nilu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments