Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi

Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan  mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana

Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan  mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana mulkin mallaka a matsayin laifi kan bil’adama, da kuma tabbatar da an biya diyya bisa ga barna da cin zarafi da aka yi wa al’ummomin Afirka.

Taron, wanda aka gudanar a babban birnin Aljeriya, an gudanar da shi  ne bisa wani kuduri na Tarayyar Afirka (AU) da aka amince da shi a farkon wannan shekarar wanda ke kira da a yi adalci wajen biyan diyya don magance illolin siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa da suka faru sakamakon mulkin mallaka.

Ministan Harkokin Wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya ce tarihin Aljeriya a karkashin mamayar Faransa ya sanya kasar ta zama muhimmin wuri na taron. Ya jaddada cewa dole ne a dauki diyya a matsayin wajibi na shari’a, ba wata alama ta alheri ko taimako ba.

Ya kuma jaddada cewa Afirka tana da ikon neman a amince da laifukan da aka aikata wa al’ummarta a lokacin mulkin mallaka,” wanda ke ci gaba da aifar da matsaloli da koma baya a bangarori daban-daban a nahiyar sakamakon illoli na mulkin mallaka.

Tsakanin 1954 da 1962, Aljeriya ta sheda daya daga cikin yaƙe-yaƙe mafi muni da kuma zubar da jini da aka yi tsakaninta da  masu mulkin mallaka. An kashe dubban daruruwan mutanen kasar .

Attaf ya ce wahalhalun da Aljeriya ta fuskanta sun  kasance “abin koyi ne amma mai wahala, kuma ya zama wajibi ya zama mafari na soma neman hakkokin da aka saryar na al’ummar Afirka sakamakon zalunci na ‘yan mulkin mallaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments