Ali Baqiri Ya Ce: Idan Yahudawan Sahayoniyya Suna Da Hankali Ba Zasu Sake Shiga Yaki Da Lebanon Ba

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Kasar Lebanon za ta zama jahannama ga yahudawan sahayoniyya da ba zasu taba tunanin sake mamaye ta

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Kasar Lebanon za ta zama jahannama ga yahudawan sahayoniyya da ba zasu taba tunanin sake mamaye ta ba

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri ya yi nuni da cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su dauke da wasu kyawawan abubuwan tunawa a kasar Labanon, kuma hanyar rugujewar haramtacciyar kasarsu ta fara ne daga kasar Labanon, yana mai gargadin cewa: Idan har yahudawan sahayoniyya suna da tunani, to ba za su wurga kansu cikin mummunan hali, fiye da mummunan halin da suke ciki ba.

Baqiri da ya halarci zaman taron manema labarai na hadin gwiwa da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki Qasim Al-Araji a birnin Bagadaza na kasar Iraki ya bayyana cewa: Wasu na nuna damuwarsu game da yakin da ke yaduwa daga Gaza zuwa kudancin kasar Labanon, amma yahudawan sahayuniyya ba su da kyakkyawan tunani game da Lebanon musamman ganin yadda hanyar rugujewarsu ta fara daga Lebanon, inda suka dandana kudarsu a shekara 2000 da kuma shekara ta 2006. Ya kara da cewa: Idan da yahudawan sahayoniyya suna da hankali, ba za su tashi daga mummunan yanayi zuwa wani yanayi mafi muni ba, yana mai bayyana cewa: Lebanon za ta zama jahannama ga ‘yan sahayoniyya da ba zasu taba mafarkin komawa cikinta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments