Al-Houthi : Murkushe Zanga zangar Goyan Bayan Falasdinawa Da Daliban Amurka Ke Yi Abun Kunya Ne

Jagoran kungiyar Ansarullah, da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a kasar Yemen, ya ce murkushe zanga-zangar lumana da daliban jami’o’I Amurka ke yi,

Jagoran kungiyar Ansarullah, da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a kasar Yemen, ya ce murkushe zanga-zangar lumana da daliban jami’o’I Amurka ke yi, domin nuna goyan baya ga falasdinawa abin kunya ne ga mahukuntan Amurka.

Yayin da yake gabatar da jawabi a yammacin jiya Alhamis, Abdul Malik Badr al-Din al-Houthi ya ce zanga-zangar lumana ta daliban Amurka na kyamar Isra’ila na ci gaba da yaduwa a duk fadin kasar, kuma hakan manununiya ce ta yadda Amurkawan basu gamsu da siyasar karya ta hukumomin Amurka.

An fara zanga-zangar daliban Amurka a ranar 17 ga Afrilu a Jami’ar Columbia da ke New York; Daliban da suka gudanar da zanga-zangar sun yi kira ga jami’ar da ta yanke hulda da hukumomin Isra’ila da ke da hannu a yakin Gaza.

Al-Houthi ya soki fuska biyu na Amurka game da ‘yancin fadin albarkacin baki ya kuma tunatar da cewa: Kungiyar dalibai ta Amurka ta yi kira ne kawai da a kawo karshen yakin Gaza.

A halin da ake ciki dai Zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa na ci gaba da yaduwa a jami’o’in Amurka.

Sama da mutum 1000 ne aka kama cikin mako biyu sanadiyyar zanga-zangar, a cewar rahotannin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments