Al-Adu Da Ci Gaban Addinin Musulunci A Tarihi 26

26-Assalami alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-Adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, shiri wanda

26-Assalami alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-Adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, shiri wanda yake kawo maku irin ci gaban da masana a tsawon tarihin addinin musulunci suka kawo na ci gaba a dukkan bangarorin rayuwar bil’adama a doron kasa tun bayyanar addinin musulunci har zuwa yau, wanda ni tahir amin nake kawo maku sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu acikin shirimmu na yau.

////…Madalla, idan masu sauraro suna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da magana a kan ilmin likitanci da magunguna, kuma mun ambaci manya manyan sunanyen likitoci musulmi da aka yi a tarihin addinin musulinci. Wadanda suka hada da Zakariya Razi a fannin likitanci.

Mun ce Sau da dama ba’a rubuta magungunan cutar da ake fama da ita a kasashen musulmi a littafan da aka tarjama ba.

A matsayin misalin da mukaga Zakariya Razi ya kawo cututtuka da maganinsu har guda 700 a cikin littafinsa Hawi, al-hali   Dioscorides wani masanin ilmin likitanci da magunguna na Girka ya kawo 500 ne kacal.

Sannan mun ce, muna iya cewa a karshen karni na 3 hijiriyyah asasin binciken ilmin likitanci na Hippocrates da Galen sun zo karshe. Sai dai a dai dai lokacinne, wani nau’I kuma sabon ilmin likitanci wanda ake kira “Tibbun Nabawi’ ya bayyana.

Manufar bayyanar wannan sabon salon magance cututtuka shi ne bada dama ga sabon salon aikin likita wanda ba na masana girkawa ba gabatar da ayyukansa.

Wadanda suka rubuta irin wadan nan littafai malaman addini ne, tunda su suka san manzon All..(s). Suna ganin hanyar jinya ta amfani da ruwayoyin da aka karbo daga masu ruwaito hadisai daga manzon All..(s). da kuma ayoyin Alkur’ani maigirma yafi ra’ayin masana ilmin likitanci na girka.

Mun ce ya rubuta littafai ko risalah fiye da  200, wadanda suka shafi Ilmin likitanci, magunguna, falsafah, hikimar dabi’ah, da taurari da sauransu.

Sannan a cikin wadan nan littafan, kimani 100 daga cikinsu kan ilmin likitanci da magunguna ne.

Littafin Hawi da kuma wanda yake kira Al-Mansuriy sune mafi muhimmanci daga cikinsu. A cikin littafin ya yi bayanin abinda ya lura da su a cikin ayyukan da yake yiwa marasa lafiyansa.

Wannan littafin ya fi ko wani littafin ayyukan likitanci a lokacin, kuma yafi tattara bayanan ayyukan likitanci a zamanin. A halin da muke magana kusan rabin wannan littafin yana nan.

Ya raba littafin gida biyu, bangare sanin ilmin kawai da kuma aiwatar da ayyukansa. Wanda ya zama kekyawar misalin ilmin likitanci ga wanda yake son koyonsa a lokacin.

A cikin shirimmu na yau zamu ci gaba da kawo maku irin ayyukan da Zakariyya Razi yayi a fannin likitanci. Wanda a yau zamu fara da aikinsa na Littafin Almansuri, dangane da aikin likitanci.

Wannan shi ne littafin koyon aikin likitanci na farko da aka buga a kasashen Turai. Littafin Al-Mansuri, littafi ne, na koyon aikin likitanci, bai da girma soasi, kuma yana dauke da takaitaccen ilmin koyon aikin likitanci, wanda shi Zakariya Razi ya rubuta ya kuma bada shi kyauta ga Sarki Abu Saleh Mansur dan Ishaq hakimin Ray na lokacin.

Razi ya rubuta littafin Al-Mansuri, gida biyu, kashi na farko yana magana kan sanin jikin bil’adama, da kuma yanda halittarsa take. Da kuma yanda magunguna suke tasiri a jiki. Tsabta, da rabe-raben kuraje, da nau’o’in guban kwari, da kuma cututtuka. An tarjama wannan littafin cikin harshen turanci sannan an buga shi sau da dama. Wanda ya watsa wannan littafin a kasashen turai shi ne  Gerard Carmonai a shekara ta 1114, da shekara ta 1186m. An tarjama shi ne a shekara ta 1510m.

Razi yana da wani littafi dangane da Kyanda da cutar ƙaiƙayi, yana daga cikin littafansa mafi tsufa kuma mafi muhimmanci dangane da wadannan cututtuka guda biyu.

Zakariya Razi shi ne likita na farko da muka sani wanda ya rarrabe tsakanin cutar Kyanda da kuma kaikayi. Sai kuma littafin ‘Al-Jadari” Ta’ajjub wa Tahsinu Gharibuha” yana daga cikin tsoffin littafan likitanci. Kuma yana daga cikin littafin likitanci masu muhimmanci wanda musulmi suka samar. Sharhin wadan nan littafai guda biyu, wanda Razi yayi masu yayi kama da wanda ake karantawa wannan zamanin.

Masu binciken tarihin likitanci, daga ciki har da Neuburger kamar yadda ya zo cikin littafin (tarihin likitanci) sun bayyana cewa, wadannan littafan suna daga cikin littafan likitanci mafi amfani wadanda musulmi suka rubuta.  

Neuburger ya ce “A gaskiya, ko ta ina ake magana, wannan littafin kawa ce ga rubuce rubucen musulmi a fagen ilmin likitanci.

An tarjama wannan littafin na Razai a tsakanin shekara ta 1498 da kuma shekara ta 1866M. Kuma an buga shi har sau 40 a cikin wannan lokacin.

A birnin londan na kasar Burtania an buga shi a shekara ta 1896M. Sai kuma littafin “Man La Yahduruhu Attabib” wanda sharyatarwa ne, ga gama garin mutane, kan yanda zasu kula da cututtuka a inda basu da likita.

Sai kuma likita babba, a tarihin addinin musulunci wanda sunansa ya je ko ina a duniya, wato Abu Ali Hasain bin Abdull..bin Sina (370-428) kamariyya. Wanda ake wa lakabi da Sheikh Arra’iss. Malamin falsafa, likita, masanin ilmin lissafi, ba irane. An haife shi a kauyen Afshaneh na garin Bukhara, sannan mahaifinsa Abdullahi kuma mutumin garin Balkh ne na kasar Afganistan. A farkon rayuwarsa Ibn Sina ya fara da karatun addinin, wadanda suka hada da Alkur’ani mai girma, ilmin ladubba masu kyau, fikihu, lissafin kasar Indiya. Sannan ya dan shekara 10 a duniya ya haddace al-kur’ani mai girma.

Sannan wannan babban malamin yana dan shekara 16 a duniya ya zama babban likita mashahuri cikin mutane. Sai dai kamar yanda likitoci suke, shi yana daukar kansa karamin mutum ne.

A lokacinda Nuhu dan Sarki Mansur Somoni ya yi rashin lafiya sannan likitoci a zamanin suka kasa warkar da shi, amma Abu Ali Sina ya zo da wasu dabarbarunsa ya kuma yi masa jinya har ya warke, sai sunan sa ya watsu har ya kai ga sarakuna kamar Shi hakiman Ray duk suka fara sanin matsayinsa.

Bayan haka ne Hakimi mansur ya bawa ibnu Sina damar amfani da dakin ajiyar littafai na Samunawa a zamanin. Ibn Sina ya yi amfani da wannan damar da ya samu ya karance dukkan littafn da suke cikin dakin ajiyar littafai na sarki ko hakimi mansur a cikin shekaru biyu.

Abu Ali Sina yana faɗa game da karatunsa a wannan ɗakin karatu, yana cewa: Na ga wata faadaa mai ɗakuna da yawa, ko wane ɗaki yana ɗauke da akwatuna cike da littattafai waɗanda aka keɓe ga wani fanni na ilmi. Wani dakin littafn adabin larabci, wani Fikihu, wani, likitanci, da sauran ilmomin da aka sani a cikin al-umma. An ga jerin sunayen littafan magabata, na daukesu daya bayan daya na karanta, duk littafin da nake so a cikin dakunan zan dauka in karanta. Na ga wasu littafai wadanda ban taba ganinsu ba, wasun kuma ban ma taba jin sunayensu ba. Ina dan shekara 18 na gama karatun dukkan fannonin ilmin da suke cikin dakunan ajiyar littafan. Na sannan kusan dukkan fannonin ilmi a zamanin. Daga lokacin kuma ba abinda yake boye a gareni.

Babbanci kawai shi ne hadda ta karu  kuma ta kara yawa,  kuma saboda haka a yau tunanina ya kara fadi  ilimina ya girma sosai”

Ibn Sina shi ne likita fami shahara a zamanin daukakar addinin musulunci, kuma littafin mafi muhimmanci da ya rubuta a fannin likitanci shi ne mai suna ‘Kanun”. ko (kanun Fittibbi”. Kafin haka ba’a taba samun littafi dauke da ilmin likitanci, wanda kuma ya tattara kome kamarsa ba.

Kuma ba a banza ne, bayan tarjamar littafin ‘Kanun’ zuwa harshen turanci, likitoci da malaman kiwon lafiya a turai sauka sanya shi a matsayin littafi na asali a koyon aikin likitanci a jami’o’insu ba.

Wani abin mamaki shi ne, littafin Kanun na Ibn Sina, shi ne wani bangarensa yana magana ne dangane da sabanin da ke tsakanin  Galen da Aristotle.

Galen ya ganin cewa kwakwalwar ɗan adam ita ce tushen jijiyoyi gabbai da kuma ƙarfinsu, sannan zuciya kuma ita ce tushen jijiyoyin jini.

Amma Aristotle ya na ganin cewa zuciya ba wai kawai ita ce tushen jijiyoyin jini ba, sai dai nan ne tsakiyar rai da kuma tushen dukkan ayyuka  jikin ɗan adam yake, kama da aikin narkewar abinci a ciki, samar da jini, tare da motsawar rai.

Dangane da wannan, ibnu Sina, bayan gabatar da ra’ayoyin Galen da Aristotle, ya ba wa Aristotle gaskiya.

Masu sauraro nan zamu dasa aya  a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

===============================================.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted