Kasar Afirka ta Kudu ta nuna matukar damuwarta kan kisan gillar da aka yi wa Hassan Nasrallah shugaban kungiyar Hezbollah ta kasar Lebonon.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Pretoria ta bayyana matukar damuwar ta biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin kisan gilla, sannan ta kuma yi nadamar jerin hare-haren da Isra’ila ta kai kan birnin Beirut.
Ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu na bayyana goyon bayanta ga Lebanon, da kuma yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa.
Kiran da ya yi daidai da wanda Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi, a Majalisar Dinkin Duniya, kwanaki kadan da suka gabata.
Kusan shekara guda, Pretoria na ci gaba da yin Allah wadai da ayyukan Tel Aviv, musamman kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza.
Kasar ce ta fara shigar da karar Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa, inda ta yi imanin cewa an karya yarjejeniyar kisan kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya.
A yanzu gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce tana tsoron “babban rikici a yankin” idan ba a yi amfani da dokokin kasa da kasa ba.