Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce kasarsa na binciken wani jirgin sama da ya kawo ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 153 kasar ba tare da takardun shiga ba.
“Wadannan mutane ne daga Gaza wadanda, ta wata hanya, suka tsinci kansu cikin jirgin sama da ya tashi daga Nairobi (babban birnin Kenya) kafin su iso nan,” in ji Ramaphosa ga manema labarai, yana mai cewa hukumomin leken asiri da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar suna binciken lamarin.
A ranar Alhamis, Afirka ta Kudu ta ba Falasdinawan su 153 mafaka ta kwanaki 90, duk da cewa an hana su shiga saboda sun gaza amsa tambayoyin da aka musu kuma fasfo dinsu ba su da tambarin tashi, ko tikitan komawa in ji Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Afrika ta kudu a cikin wata sanarwa.
A halin yanzu, ofishin jakadancin Falasdinu a Afirka ta Kudu ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa ‘yan Falasdinu 153 sun iso ba tare da wata sanarwa ko hadin gwiwa ba.
An bayyana cewa wata kungiyar mayaudara ce ta shirya jirgin.
Ofishin jakadancin ya ce kungiyar ta yi amfani da mummunan halin jin kai na al’ummar Gaza, ta yaudari iyalai, ta karbi kudi gare su, ta samar musu tafiyar ta hanyar da ba ta dace ba, saidai kungiyar agaji ta Gift of the Givers, ta shaida wa tashar talabijin ta Afirka ta Kudu SABC cewa Isra’ila ce ke da alhakin shigar ‘yan gudun hijirar Falasdinawa cikin kasar ba bisa ka’ida ba.