Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi

Rahotanni da suke fitowa daga birnin Pretoria sun ce, adadin mutanen da su ka kwanta dama sanadiyyar bude wuta ta kan mai uwa da wabi,

Rahotanni da suke fitowa daga birnin Pretoria sun ce, adadin mutanen da su ka kwanta dama sanadiyyar bude wuta ta kan mai uwa da wabi, sun kai 11 daga cikinsu har da karamin yaro dan shekaru uku.

Jami’an ‘yan sandan kasar ta Afirka Ta Kudu ne su ka sanar da cewa an bude wutar ne a cikin wani gidan shan barasa dake birnin Pretoria a jiya Asabar. Haka nan kuma sun sanar da kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a abinda ya faru.

Kananan yara uku ne dai kisan ya hada da su, biyu daga cikinsu shekarunsu uku-uku ne, sai daya mai shekaru 12. Kuma da akwai wata buduruwa ‘yar shekaru 16 da ita ma lamarin ya rutsa da ita.

Wani sashe na sanarwar ya ce da akwai wasu  mutane 14 da su ka jikkata sanadiyyar bude wuta na daban da aka yi a garin Solsifl.

Kasar Afirka Ta Kudu dai tana fuskantar matsaloli irin wannan na bude wuta akan mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted