Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinawa ta sanar da cewa, a cikin shekara daya na yakin Gaza, sojojin HKI sun kashe ‘yan jarida da adadinsu ya rubanya wadanda aka kashe a duniya baki daya har sau biyu.
A bayanin da kungiyar ‘yan jaridar ta Falasdinawa ta fitar ya bayyana cewa; Yadda Sojojin “ Isra’ila” Suke yi wa ‘yan jaridar kisan gilla na ganganci saboda su hana su daukar laifukan da suke tafkawa, ba zai wuce ba tare da hukunci ba.
Haka nan kuma kungiyar ta ce, kisan ‘yan jarida da kuma kisan kiyashi da ake yi wa mutanen Gaza, shi ne barna mafi girma da ta faru a tsawon tarihin aikin jarida a duniya.
Har ila yau, bayanin ya ce, yawan ‘yan jaridar da sojojin mamayar su ka yi wa kisan gilla sun kai 183 da hakan yake nufin rubanyawa har sau biyu na yawan ‘yan jaridar da aka kashe a duniya a cikin shekara daya.