Adadin shahidai a zirin Gaza ya kai mutane dubu 37 da 372

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da sabuwar kididdigar shahidan Zirin Gaza tare da bayyana cewa: daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da sabuwar kididdigar shahidan Zirin Gaza tare da bayyana cewa: daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa yau mutane dubu 37 da 372 ne suka yi shahada a wannan yanki.

Kamfanin dillancin labaran IRNA  ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sama cewa, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a ranar Talata cewa, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata gwamnatin sahyoniyawan ta aikata wasu sabbin laifuka guda uku a yankuna daban daban na yankin a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, inda yayi sanadiyyar shahadar mutane 25, tare da jikkatar wasu 80.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta kuma sanar da sabon adadin mutanen da suka jikkata na wadannan laifukan da suka kai dubu 85 da 452.

Ma’aikatar ta kara da cewa an bar gawawwakin shahidai da dama a karkashin baraguzan ginin, wasu kuma an bar su a gefen titi, wadanda kungiyoyin agaji ba sa iya isa wuraren da suke domin dauke su, sakamkon ci gaba da kaddamar da hare-haren da Isra’ila ke yi a yankunan.

Tashar  Aljazeera ta bayar da rahoton  cewa, tun a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, lokacin da gwamnatin sahyoniyawan ta fara kai munanan hare-hare a kan yankin na zirin Gaza tare da goyon bayan Amurka, dubun dubatan Palasdinawa wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne suka yi shahada da kuma jikkata,sannan wadannan hare-haren sun rusa ababen more rayuwa na Zirin Gaza Wani bala’i da ba a taba ganin irinsa ba a wannan yanki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments