A Myanmar adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar ya karu zuwa 3,354 a gwamnatin mulkin sojan kasar.
Girgizar kasar ta kuma jikkata wasu mutane 4,850, sannan akwai wadanda har yanzu kuma ba a gansu ba.
Bayanai sun ce bala’in na iya kara kawo cikas ga gwamnatin mulkin sojan kasar.
Myanmar dai na cikin rudani bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2021.