Adadin Falastinawa Da Suka Yi Shahada A Gaza Ya Haura 42,600

Ma’aikatar Lafiya a yankin zirin Gaza ta sanar da cewa adadin mutanen da harin Isra’ila ta kashe a Beit Lahia da ke arewacin Gaza ya

Ma’aikatar Lafiya a yankin zirin Gaza ta sanar da cewa adadin mutanen da harin Isra’ila ta kashe a Beit Lahia da ke arewacin Gaza ya kai 87, Sanarwar ma’aikatar ta ce sama da karin mutum 40 sun raunata, ciki har da wadanda ke mawuyacin hali.

Tuna bayan 7 ga Oktoban 2023, harin sojojin Isra’ila a Gaza ya halaka aƙalla Falasɗnawa 42,603, kuma ya jikkata 99,795, cewar ma’aikatar.

Wannan adadin bai hada da gomman mutanen waɗanda harin cikin daren jiya ya rutsa da su ba, cewar rahoton AFP wanda ya ambato masu ceto.

Jami’in na musamman na majalisar Dinkin Duniya Tor Wennesland ya yi tir da harin da Isra’ila ta kai kan garin Beit Lahiya na Gaza, wanda ya kashe gomman mutane, kuma ya yi kira da a kawo karshen hare-hare kan farar-hula da kare Falasɗinawa da suka tagayyara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments