Abdumalik Alhusi Ya Ce, A shirye Suke Su Koma Yaki Idan HKI Ta Ci Gaba Da Keta Wutar Yaki

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya  yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya  yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada.

Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga cikin manyan shugabannin Ansarullah, ya kara da cewa, ci gaba da wanzuwar kungiyar ta Hamas yana daga cikin muhimman ayyukan da Muhammad Dhaif ya aiwatar a lokacin rayuwarsa.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Muhammad Dhaif ga kungiyar ta Hamas, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagorori abin koyi saboda ruhinsa na imani mai karfi, azama da ruhi na jihadi.

Da yake Magana akan yadda al’ummar Yemen su ka taimakawa gwgawarmayar Falasadinawa,  Sayyid Abdulmalik al-Husi, ya kara da cewa; Idan har ‘yan sahayoniya su ka koma yaki, to su ma mutanen Yemen za su koma fagen dagar taimakawa Falasdinawa.

Dangane da kasar Lebanon ma Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi yabo akan yadda al’ummar kudancin kasar suka koma garuruwansu da hakan yake a matsayin babban jihadi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments