Iran da Oman sun jaddada aniyarsu ta kara fadada alakar da ke tsakaninsu

Ministocin harkokin wajen Iran da Omani sun bayyana aniyar kasashensu na yin aiki tare don kara fadada alakar da ke tsakaninsu. An yi musayar kalaman

Ministocin harkokin wajen Iran da Omani sun bayyana aniyar kasashensu na yin aiki tare don kara fadada alakar da ke tsakaninsu.

An yi musayar kalaman ne a wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Abbas Araghchi da Badr Albusaidi a ranar Litinin.

Albusaidi ya yi ishara da kulawa ta musamman daga Sultan Haitham bin Tariq na Omani game da batun dangantakar da ke tsakanin Oman da Iran, da kuma yaddaa alakar take kara samun bunkasa a dukkanin matakai.

Ya bayyana shirinsa na yin aiki kafada da kafada da takwaransa na Iran domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin bangarorin biyu.

A nasa bangaren, Albusaidi ya taya Araghchi murnar bashi matsayin babban jami’in diflomasiyyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana shirinsa na yin hadin gwiwa da cudanya da jami’in Oman dangane da batutuwan da suka shafi cin moriyar juna a bangarorin biyu, da na shiyya-shiyya, da kasa da kasa.

Da yake ishara da kalubalen da ke fuskantar yankin yammacin Asiya, ya ce, ci gaba da tuntubar juna da hadin gwiwa tsakanin kasashen a fannoni daban-daban, gami da batutuwan da suka shafi yankin, zai taimaka wajen warware matsalolin da ake fama da su.

Majalisar Dokokin Iran ta amince da Araghchi a matsayin ministan harkokin wajen kasar a ranar Laraba. Ya karbi mukamin ne daga hannun mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Ali Bagheri Kani, wanda ya rike mukamin babban jami’in diflomasiyyar Iran na wani dan lokaci bayan rasuwar  tsohon ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan Mayu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments