Gwamnatin gabashin Libiya ta sanar da rufe dukkan wuraren da ake hako mai tare da dakatar da ayyukan hakowa da fitar da man
Gwamnatin gabashin Libya ta sanar a ranar Litinin cewa, za a rufe dukkan wuraren da ake hako man fetur, kuma an daina hakowa da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, sai dai babu wata sanarwa da gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita a Tripoli ta fitar.
Kamfanin mai na kasar da ke kula da albarkatun mai na kasar Libiya ma bai tabbatar da hakan ba.
Kamfanin mai na Al-Waha da ke da alaka da Kamfanin Mai na kasa, ya ce yana da niyyar rage hako man sannu a hankali tare da gargadin daina hakowa gaba daya.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a shafinsa na yanar gizo, “Kamfanin mai na Waha ya yi gargadin cewa ci gaba da zanga-zanga da matsin lamba zai haifar da dakatar da hako mai, kuma kamfanin zai fara rage yawan man da ake hakowa sannu a hankali tare da yin kira ga hukumomin da suka dace da su shiga tsakani don ci gaba da yin hakan.