Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Sudan Ya Ce: Aiwatar Da Yarjejeniyar Jedddah Ita Ce Mafitar Kasarsa

Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan kuma babban hafsan hafsoshin sojin kasar ya bayyana makomar yakin Sudan Kwamandan sojojin Sudan Janar Abdul Fattah al-Burhan,

Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan kuma babban hafsan hafsoshin sojin kasar ya bayyana makomar yakin Sudan

Kwamandan sojojin Sudan Janar Abdul Fattah al-Burhan, ya tabbatar da cewa: Yakin Sudan zai ci gaba da gudana har sai an aiwatar da bukatun sojojin Sudan kasar, yana mai cewa, sakamakon zaman dandalin birnin Jeddah na kasar Saudiyya shi ne tushen duk wata tattaunawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.

A taron manema labarai da ya kira a birnin Port Sudan, Al-Burhan ya ce,   tabbas Sudan ba ta aike da tawaga daga sojoji ko jami’an gwamnatin kasar zuwa Geneva ba, kamar yadda Amurka ta so, wanda ke nuni da cewa sakamakon dandalin Jeddah shi ne tushen ko wane ce tattaunawar da ta shafi yakin Sudan.

Al-Burhan ya kuma tabbatar da cewa sojojin Sudan za su yi yaki na tsawon shekaru dari, sai dai idan ba a biya musu bukatunsu ba, da kuma komawa kafin watan Mayun 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments