Shaikh Zakzaky: Taro a kan hanyar Karbala hujja ce ta nasarar yunkurin Imam Hussain (a.s.)

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya jaddada cewa duk wani matsayi na goyon bayan Palastinu ya samo asali ne daga tafarkin koyarwa

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya jaddada cewa duk wani matsayi na goyon bayan Palastinu ya samo asali ne daga tafarkin koyarwa ta Imam Hussain (a.s) .

Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya bayyana hakan ne a yayin taron rufe tattakin da aka yi wa taken ‘Kiran Al- Aqsa’ a kan hanyar masu ziyara Karbala , yana mai nuni da cewa al’ummar Palastinu suna yakar dukkanin ma’abuta girman kai na duniya, ya kuma ce: gwamnatin mamaya duk da irin goyon bayan da take samu daga manyan kasashen duniya babu abin da ta cimma face kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Sannan kuma a yayin tattakin Arbain a kasar Iraki ya jaddada cewa guguwar Al-Aqsa wata nasara ce ga Gaza tun daga lokacin kaddamar da wannan farmaki, inda ya ce: tsayin daka da imanin Palasdinawa ya canza ra’ayin duniya kan Musulunci.

Yayin da yake bayyana cewa Imam Husaini (a.s.) ya samu nasarar sauya tunanin duniya a yunkurinsa, yana mai nuni da cewa: Dukkan wadannan mutanen da za su je Karbala suna masu karba kiran Imam Husaini (a.s.) ne.

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya jaddada cewa tarin jama’a a halin yanzu wata shaida ce ta nasarar da aka samu a kan Takobin azzalumai, inda ya ce: “Na tilasta wa kaina in kalli al’amuran Gaza masu zafi a kowace rana, duk kuwa da cewa abin yana tayar da hankali.”

Yayin da yake jaddada cewa duk wani matsayi na goyon bayan Palastinu ya samo asali ne daga mazhabar Imam Husaini (AS), inda ya ce: Taron da masu ziyara suka yi a hanyar Karbala a yau shaida ce ta nasarar da yunkurin Imam Husaini (AS) ya samu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments