Gaza : ‘Yan Fafatuka A Afrika Ta Kudu Na Son Kasar Ta Sanyawa Isra’ila Takunkumi

‘yan fafatuka A Afrika ta Kudu, sun ce yunkurin da kasar ke yi na tuhumar Isra’ila a kotun kasa da kasa bai wadatar ba, inda

‘yan fafatuka A Afrika ta Kudu, sun ce yunkurin da kasar ke yi na tuhumar Isra’ila a kotun kasa da kasa bai wadatar ba, inda suka bukaci gwamnatin ta yanke duk wata huldar kasuwanci da Isra’ila tare da sanyawa gwamnatin kasar takunkumi.

Da gawayin Afirka ta Kudu ana samar da wutar lantarki kashi 15% a tashar wutar lantarki ta Isra’ila, kuma hakan na bukatar dakatar da shi nan take, sabdoa yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Afirka ta Kudu ita ce babbar abokiyar kasuwanci da Isra’ila a Afirka, kuma a cikin watanni 8 da suka gabata, ta aika sama da tan 500,000 na gawayi zuwa ga mulkin zalunci, wanda ya sanya ta cikin manyan kasashe uku masu samar da kayayyaki a duniya.

Ta hanyar fitar da gawayi zuwa Isra’ila, muna ba da taimako da tallafawa wannan kisan kare dangi a Gaza, inji ‘yan fafatukar na Afrika ta Kudu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments