Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce Isra’ila ta ketare “dukkanin layuka ” ta hanyar kai farmaki kan kudancin Beirut, yana mai cewa kungiyar za ta yanke shawarar kai karin hare-hare na ramuwar gayya kan gwamnatin Isra’ilar a nan gaba.
Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa kai tsaye ta gidan talbijin yau Lahadi bayan da kungiyar gwagwarmaya ta harba daruruwan rokoki da jirage marasa matuka zuwa Isra’ila a matsayin ramuwar gayya kan kisan babban kwamanda Fuad Shukr.
Ya ce kungiyar Hizbullah ta kai hare-haren ramuwar gayya na baya bayan nan, maimakon kan farar hula a wuraren sojojin Isra’ila, wanda ya kira “Operation Arbaeen”.
Har ila yau shugaban na Hizbullah ya ce manyan wuraren da aka kai hari su ne sansanonin leken asiri da kuma sansanonin tsaron sama, ya kara da cewa kungiyar masu fafutuka ta yanke shawarar kai hari kan sansanin leken asirin sojan Glilot da ke kusa da birnin Tel Aviv.
Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa, Isra’ila na kokarin boye irin hasarar da aka yi mata sakamakon harin ramuwar gayya na kungiyarsa.
Shugaban kungiyar ta Hizbollah, Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa, kungiyar Hizbullah ta jinkirta kai hare-haren daukar fansa kan Isra’ila saboda tattaunawar tsagaita bude wuta da ake yi a zirin Gaza, da kokarin da take yi na ganin an kawo karshen yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi kan yankin da aka yi wa kawanya.