Mai gabatar da kara a kotun kasa da kasa ta ICC Karim Khan ya bukaci alkalai wadanda abin ya shafa a kotun, sun gaggauta fitar da sammacin kama shuwagabannin HKI saboda zarginsu da aikata laifukan yaki kan al-ummar Falasdinu a zirin Gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Khan dan kasar Burtaniya yana fadar haka a yau Asabar, ya kuma fara fadar haka ne tun kimani watanni uku da suka gabata, kan cewa ya tabbata a gareshi kan cewa shuwagabannin HKI sun aikata laifukan yaki a kan al-ummar Falasdinu a Gaza, kuma ya gabatar da hujjoji da suke tabbatar da haka.
Don haka tun lokacin ya bukaci majalisar alkalai wadanda abin ya shafa a kotun su fidda sammacin kama shuwagabannin HKI, wadanda suka hada da firai ministan kasar Benyamin Natanyahu.
A cikin watan Mayun da ya gabata ne Karim Khan ya tabbatar da cewa shuywagabannin HKI, sun yi amfani da yunwa a matsayin makami a kan mutanen Gaza, wanda laifin yaki ne babban wanda yake bukatar a gurfanar da shuwagabannin da suka yi haka a gaban kuliya.